2 Corinthians 9

1Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka. 2Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki. 3Amma ina aika ʼyanʼuwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan alʼamari ta zama a banza, sai dai domin yǎ zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance. 4Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba—kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku. 5Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ʼyanʼuwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za ta zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.

Shukin Yardar Rai

6Ku tuna fa: Duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7Ya kamata kowa yǎ bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba: gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. 8Allah kuwa yana da iko yǎ ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. 9Kamar yadda yake a rubuce cewa:

“Ya ba gajiyayyu hannu sake,
ayyukansa na alheri madawwama ne.”
Zab 112.9

10To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yǎ riɓanya shi, yǎ kuma yawaita albarkar ayyukanku na alheri. 11Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za ta zama sanadin godiya ga Allah.

12Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi naʼam da bisharar Kiristi, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14A cikin adduʼarsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!

Copyright information for HauSRK